Hare-haren da ake zargin Fulani da kaiwa a wasu sassan kasar Najeriya musamman a kudancin Kaduna da ya kan haddasa asarar rayuka ya sa mahukunta sun tashi tsaye.
WASHINGTON, DC —

Sojojin Najeriya sun kai binciken kwakwaf kan garin Laduga cikin karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna inda suka yi awongaba da Fulani ashirin da biyar. Yawancin mazauna garin Laduga Fulani ne.
Sojojin sun auka garin ne da asubahin Lahadi suka yiwa garin kawanya abun da wasu daga cikin Fulanin garin suka ce ya sabawa doka. Ardo Toro Bello yace sojojin da suka shiga garin sun wulakantasu kana suka yi gaba da mutane ashirin da biyar. Yace hatta hakiminsu sai da sojojin suka yi masa tsirara. Sun kuma shiga gida gida suna bincike. Har cikin masallaci sun shiga domin yin bincike. Bello yace mutanen da aka kama basu san inda aka kaisu ba.
Korafin mutanen shi ne gwamnati ta sa ido a daina kama masu mutane domin su basu taba taba wani ba ko wata kabila hatta ma kabilun dake makwaftaka da su.
To saidai mai magana da yawun rundunar soja dake Kaduna Kanal Abdul yace rahotannin da suka samu sun nuna cewa ana shirin kai harin ramuwar gayya.Dalili ke nan da sojoji suka je garin Laduga. Inji Kanal Abdul binciken da suka yi ya yi sanadiyar kama wasu makamai da dama.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5