Yace sun zauna da gwamnonin kuma ta gefensu suna kokari su ga an kawo karshen tashin tashinar. Yace ana zagayawa ana gayawa mutane su zauna lafiya da junansu yace su ma a Taraba suna nan suna kokari. Yace duk su gwamnonin sun fahimci juna domin dama an basu hakin mutanen kuma yakamata su rikesu a matsayin amana su kuma tabbatar sun zauna lafiya.
To saida kawo lokacin da gwamnonin suka yi taronsu ana samun harin sari ka noke a wasu yankunan jihar Taraba inda wasu ke ketarowa daga jihohin dake makwaftaka da ita su kai hari cikin kauyuka musamman a yankin Ibi. Isiyaka Adamu shugaban karamar hukumar Ibi ya bayyana matakan da suke dauka domin harin sari ka noke da ake kaiwa kan kauyukansu. Yace sun sanarda gwamnatin jiha kuma an kara masu jami'an tsaro dake yin sintiri yanzu. Sai dai yace akwai dazuzuka munana da jami'an tsaro basa iya shiga. Cikinsu ne wasu kauyuka suke da ake kaima hari.
Masarautar Donga dake kudancin jihar ta shirya taron sulhu tsakanin Fulani da Tibabe domin samun zaman lafiya. Sarkin Donga ya kirawo shugabannin Fulani da na Tibabe da jami'an tsaro inda ya nemi su zauna lafiya a masarautarsa.
Ga karin bayani