Yayin da ake cigaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin wakilai masu halartar taron kasa inda wasu daga arewacin kasar ke barazanar kauracewa taron, wasu gwamnoni da ma wasu shugabannin kungiyoyi sun soma kiran wadanda suke zauran taron su kai zuciya nesa.
Kalamun daya daga cikin wakilan taron, Lamidon Adamawa Dr. Barkindo Aliyu Mustapha yayi na cewa masarautarsa tare da yankin Adamawa ka iya komawa kasar Kamaru ya haddasa cecekuce da muhawara a kasar. Yayin da wakilan kudancin kasar ke mayarda kalamu masu zafi kan furucin Lamidon wasu kuma daga arewa cewa su ke dole a yi kafin ta natsu muddin ana son Najeriya ta cigaba da kasancewa kasa daya.
Mallam Yakubu Bello na kungiyar sasanta al'umma da kawo zaman lafiya na ganin akwai abun dubawa a kalamun Lamidon Adamawan. Yace kalamun Lamido sun taso ne domin ana ganin 'yan kudu suna son su yi anfani da taron ne su kawowa arewa barazana. Yace ba'a son a fadawa juna gaskiya domin shugabanni sun san matsalar kasar kuma ba a irin taron kasa za'a warwaresu ba. Yace yakamata a yi adalci kana a dauki mataki kan cin hanci da rashawa. Abu na gaba a tabbatar doka ta yi aiki kan kowa babu nuna son kai. Idan an yi wadannan abubuwa komi zai tafi daidai.
Idan an zabi shugaba kuma ya zo yana nuna bangaranci ko addinanci to ko ba za'a samu zaman lafiya ba. Yace a duba a Benue akwai rigima tsakanin Tiv da Idoma,haka tsakanin Tiv da Fulani. A Adamawa rigima na nan da Fulani da kananan kabilu. A Borno ma Kanuri basa shiri da kananan kabilu. Domin haka rigingimu na nan koina. Koda kowace karamar hukuma zata zama jiha za'a samu matsala muddin babu adalci.
Shi ma gwamnan Adamawa yace muddin ana son zaman lafiya da cigaba to dole a yiwa kowa adalci. Ya kira ga kasar cewa a sake rayuwa. A bar hainci kuma a bar zalunci. A baiwa kowa hakinsa shi ne kadai zai kai kasar cin nasara.
Ga karin bayani.