NIAMEY, NIGER - To sai dai masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na kallon abin tamkar wata dabara ta neman wuri, a daidai lokacin da manyan kasashen duniya ke rige-rigen kulla hulda da nahiyar Afrika.
A yayin taron kare gandun daji da rukukin itace na 'One Forest Summit', wanda kasar Gabon ta shirya da hadin gwiwar Faransa da ke samun halartar shugabanin kasashen yankin Afrika ta tsakiya a jiya Alhamis, shugaba Macron ya bayyana cewa zamanin huldar nan ta 'France Afrique' wato zamanin huldar uwar daki da ‘yan korenta ya wuce.
Wadannan kalamai wata dabara ce da ake ganin shugaban na Faransa ya bullo da ita da nufin maida martani ga masu zargin kasar da ci gaba da yi wa kasashen Afrika mulkin mallaka a kaikaice, saboda haka ba abin da zai canza inji mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abass Moumouni.
Domin wanke kasarsa daga zargin katsalandan a harakokin cikin gida na kasashen Afrika, shugaba Macron ya ce Faransa ba ta da bangaranci. To amma mai fashin baki Moustapha Alassan ya bayyana cewa kalamai ne na neman wuri.
Wannan wata dama ce da masana ke ganin ya kamata shugabannin Afrika su yi amfani da ita don karawa nahiyar daraja da bakin fada aji a sahun kasashen duniya.
Wannan rangadi da ke matsayin karo na 18 da shugaba Macron ke zuwa Afrika daga lokacin darewarsa karagar mulki a 2017 kawo yau, ya shafi Gabon da Congo Brazaville da DRC Congo, wato Jamhuriyar Congo Demokradiya da Angola, dukkansu masu dimbin arzikin ma’adanan karkashin kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5