Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Daidaito Kan Makomar Rundunar Barkhane Da Takuba A Yankin Sahel


A karshen wani taron da ya gudana jiya laraba a birnin Paris wanda  ya sami halartar wasu shugabanin kasashen yammacin Afrika, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ayyana shirin kwashe sojojin rundunar Takuba da na rundunar Barkhane daga Mali.

Daga bisani ya ce za a girke su a jamhuriyar Nijer domin ci gaba da yaki da ta’addanci a yankin Sahel matakin da tuni ta fara haddasa cece-kuce a tsakanin jama’ar Nijer.

Taron wanda ainihi aka shirya da nufin duba makomar rundunar Takuba ta hadin guiwar sojojin kasashen Turai da takwarorinsu na rundunar Barkhane masu sansani a Mali ya biyo bayan tankiyar diflomasiyar dake kara tsananta a tsakanin hukumomin Mali da na Faransa a abinda ya kara rikicewa bayan bayyanar labarin shirin girke dakarun kamfanin Wagner na Russia a Mali.

Da yake jawabi a wannan alhamis ta kafafen kasarsa Emmanuel Macron ya sanar cewa sun yanke shawarar kaura zuwa Nijer a maimakon kasashen Senegal da Cote d’ivoire da aka aiyana a can farko.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Seidik Abba masanin tsaro a yankin sahel, ya ce Nijar na kusa da Mali, shi ya sa fita daga Mali zuwa Nijar ba zai yi wuya ba. Bisa ga cewar shi, Faransa ita da kanta tana so ta zauna a cikin sahel ta cigaba da yaki.

Tuni dai masu fafitika suka fara nuna rashin amincewa da wannan mataki da suke ganin a maimakon ya magance matsalar tsaro sai dai ya kara rikita abubuwa, inji shugaban kungiyar tournons La Page Maikol Zody.

Sai dai ra’ayoyin jama’a sun sha bamban a game da wannan al’amari , wani tsohon dan majalisar dokokin kasa a karkashin inuwar jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki Honorable Abdoul-Moumouni Gousmane yace ba daga bakin Emmanual Macron ya kamata su ji kudiri da ya shafe kasarsu ba, sai dai ta bakin shugaban kasar Nijar.

Matsalar tsaro a kasar Mali wani abu ne da ya jefa miliyoyin ‘yan Nijer cikin halin kunci inda wasu suka kaura wasu suka rasa dukiyoyinsu hade da asarar dimbin rayukan mutane sanadiyar hare haren ta’addanci, to amma maido da rundunonin sojan na kasashen turai zai iya taimakawa kasar ta magance wannan damuwa.

A farkon watan nan na fabreru fadar shugaban kasar Nijer ta sanar cewa shugaba mohamed Bazoum ya yi watsi da tayin girke dakarun Barkhane da Takuba a wannan kasa lamarin da ya sa da dama daga cikin ‘yan kasa ke mamaki akan wannan sabon matsayi ko da yake kawo yanzu ba wasu bayanai a hukunce daga bangaren Nijer.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG