Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaron Faransa Ya Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar


Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar
Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar

Ministan tsaron Faransa da abokiyar aikinsa ta harakokin waje sun yi rangadi a Jamhuriyar Nijar inda aka tattauna akan batutuwan da suka hada da tsaro da ayyukan ci gaban al’umma a wani lokacin da rundunar Barkhane ke ci gab da kammala nade tarkacenta daga Mali zuwa jamhuriyar Nijar.

NIAMEY, NIGER - Tattaunawa ce ta awoyi da dama aka yi a tsakanin ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu da abokiyar aikinsa ta harakokin waje Catherine Colonna tare da ministan tsaron kasar Nijar Alkassoum Indatou da ministan harakokin waje Hassoumi Massaoudou dangane da daftarin aikin da kasashen biyu ke shirin zartarwa bayan girke dakarun Barkhane a Nijer a wani lokacin da ‘yan ta’adda suka fara yada ayyukansu zuwa kasashen gabar teku.

Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar
Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar

Bayan da suka yiwa shugaba Mohamed Bazoum bitar abubuwan da suka tsayar wadanan ministoci sun kira taron manema labarai.

Domin kaucewa cece kucen da aka yi fama da shi a baya dangane da batun shigo da dakarun ketare a Nijar, kasahsen biyu sun bayyana cewa sojojin Nijar ne ke da hurumin jagorancin al’amura a fagen daga.

Ayyukan ci gaban al’umma na daga cikin batutuwan da bangarorin biyu suka tattauna akansu a yayin wannan ganawa.

Ministar harakokin wajen Faransa Catherine Colonna ta ce a bisa umurnin shugaba Emmanuel Macron, a bana Faransa ta yanke shawarar tallafawa Nijar da million 20 na Euro a matsayin gudunmowar da ta saba bayarwa a kasafin kudaden wannan kasa wadanda daga cikinsu million 8 za a yi amfani da su wajen tanadin cimakar da za a ajiye a rumbun tsimi yayinda wasu million 8 din na daban za a yi aiki da su wajen ayyukan agajin gaugawa.

Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar
Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar

Ta kara da cewa a karkashin sabon fasalin da suka zo da shi ta hanyar hukumar samar da ci gaba ta AFD yau da safe ita da takwaranta na Nijar sun saka hannu akan wasu yarjeniyoyi biyu wadanda a karkashinsu Faransa za ta bada tallafin million 50 na euro don ayyukan samar da wutar lantarki ga al’umomin Nijar.

Tawwagar ta mambobin gwamnatin Faransa ta karkare wannan rangadi da gundumar Ouallam dake jihar Tilabery yankin da kasar ta Faransa ke gudanar da wasu ayyukan ci gaban al’umma kafin daga bisani su daga zuwa kasar Cote d’ivoire a Yammacin yau Juma’a.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Ministan Tsaron Faransa Da Abokiyar Aikinsa Ta Harkokin Waje Sun Kai Ziyara Jamhuriyar Nijar .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG