Shugabancin kungiyar na kasa ya kawar da duk shugabannin jihohi talatin da shida tare da na babban birnn tarayya Abuja.
Wannan matakin ya biyo bayan wani babban taron da kungiyar ta yi a garin Kaduna.
Ardon Zuru Alhaji Muhammad Kirwa shugaban kungiyar na kasa ya yi karin bayani. Yace sun rushe jagorancin ne saboda su zabensu aka yi. Wakilan jihohin Najeriya talatin da shida suka taru a Sokoto suka zabesu.
Saboda haka duk wanda aka zaba dole ne ya sa a gudanar da zabe a matakin jihohi saboda a zabi ingantattun shugabanni.
Dalilai biyu suka sa suka saukar da shugabannin jihohi. Na farko an samu canjin jagorancin kasa gaba daya. Saboda haka babu dalilin da zai hana a yi zabe domin yin koyi da abun da mutanen Najeriya suka yi.
Akwai shugabannin jihohi da suka kai shekaru talatin suna rike da mukaminsu. Shugabannin na kasa sun ce ba zasu cigaba da tafiya haka ba babu gyara cikin shugabanci. Yakamata a samu tantancewa kamar yadda kasar tayi.
Yakamata a yi zabe, kuma zaben mutane na kirki domin su yi aiki na gari.
Alhaji Muhammad Kirwa yace kungiyar ta kasa ta gano an zuba wasu zunubai a wasu jihohi saboda haka zabe za'a yi kowa tashi ta fisheshi. Wasu suna labewa da sunan kungiyar suna zaluntar 'yanuwansu ta wurin hada kai da hukuma. A wasu wuraren kuma zuwa su keyi suna aikata zalunci.
Ambassador Umar Faruk Ka'oje daya daga cikin iyayen kungiyar ya amince da rushe shugabancin kungiyar a matakin jihohi. Yace matakin ya yi daidai saboda za'a zabi sabbin shugabannin da zasu yi aiki tare dasu.. Yace wadanda suka yi abun kirki zasu sami dawowa.
Saidai wasu shugabannin jihohin nada tababan saukesun da aka ce an yi. Sun ce labari kawai suke ji domin ba'a aika masu da takardar saukar dasu ba.
Alhaji Haruna Boro Usaini shugaban Miyetti Allah reshen jihar Filato yace ba'a kirasu a gaya masu komi ba kuma ba'a rubuta masu ba don haka jita-jita ce kawai.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5