Shugabannin Duniya Na Allah-wadai Da "Kisan Gilla" Da Aka Yi Wa Shugaban Hamas

An kashe Ismail Haniyeh ne a kasar Iran - Yuli 30, 2024

A yau Laraba, Shugaban Turkiyya Recef Tayyib Erdogan, ya yi Allah-wadai da mummunan kisan gillar da aka yiwa amini kuma 'dan uwansa, shugaban kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa Musulmai ta Hamas, Isma’il Haniyeh.

Shugaban kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan

Erdogan ya kara da cewar, “manufar wannan abin kunyar shine yiwa gwagwarmayar Falasdinawa zagon kasa, tare da dakile karsashin ‘yan uwanmu Falasdinawan dake fafutuka a zirin Gaza, da kuma jefa tsoro a zukatan Falasdinawa.”

Haniyeh, wanda ya jima a kasar turkiya gabanin harin ranar 7 ga watan Oktoban da kungiyar hamas ta kaddamar akan isra’ila, ya kaiwa erdogan ziyarar karshe a birnin istanbul a cikin watan afrilun daya gabata.

Shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinawa Ismail Haniyeh tare da abokinsa shugaban Turkiye Erdogan a saduwarsu ta karshe a Istanbul Afrilu 20, 2024

Ita ma kasar Masar ta yi allawadai da kisan gillar da aka yiwa Shugaban Hamas Isma’il Haniyeh da wani kwamandan kungiyra Hezbollah, inda ta bayyana hakan da mummunan ci gaban daka iya yin barazanar fadadar rikici zuwa sauran sassan gabas ta tsakiya.

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar wajen masar tace zafafa hare-haren da Isra’ila ta yi a kwanaki 2 da suka gabata ya sake rikirkita tattaunawar tsagaita wuta a yakin da ake yi tsakanin Isra’ilar da kungiyar Hamas.

Falasdinawa-Hamas-Ismail Haniyeh

Har ila yau, a yau Laraba, kasar Iraki ta yi Allah-wadai da kisan inda ta yi gargadin cewa hakan na barazana ga zaman lafiya a yankn Gabas ta Tsakiya.

Sanarwar da Ministan Harkokin Wajen Iraki ya fitar ta bayyana kisan da “yiwa dokokin kasa da kasa hawan kawara tare da yiwa zaman lafiya da tsaron yankin barazana.”

AFP