Wannan shine dare na biyu a jere da yankin tsakiyar garin Deir al-Balah dake kusa da sansanonin ‘yan gudun hijra ke fuskantar munanan hare-hare, a daidai lokacin da masu shiga tsakani daga Amurka da Masar da Qatar harma da jami’an gwamnatin Isra’ila suka hadu a babban birnin Qatar, Doha, domin tattaunawa akan ci gaba da aiwatar da yarjejeiyar da zata kai ga tsagaita bude wuta tare da sakin fursunoni wacce ta jima tana cijewa.
A‘yan kwanakin baya-bayan nan alamu na nuni da yadda Isra’ila da kungiyar Hamas ke rage burin da suke da shi, sai dai har yanzu akwai sauran matsala.
Hare-haren na safiyar yau Laraba sun lalata gidaje uku a sansanin ‘yan gudun hijra na Nuseirat, inda suka hallaka mutane 12 ciki har da kananan yara 5, a cewar hukumomin asibitin Shahidai na al-aqsa, inda aka garzaya da wadanda harin ya rutsa dasu.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na AP ya kirga gawawwakin.
Hari na 4 da aka kai da safiyar yau Laraba ya hallaka manyan maza hudu, da mata uku da wani karamin yaro sa’ilin da aka kai hari wani gida a Deir al-balah, yankin dake cikin tudun mun tsirar da Isra’ila ta umarci Falasdinawa su nemi mafaka yayin da take cigaba da kaddamar da hare-hare a sassan zirin Gaza da dama.
Hare-haren cikin daren na zuwa ne sa’o’i bayan da jiragen yakin Isra’ila suka afkawa kofar wata makaranta dake baiwa iyalan da suka rasa matsugunansu mafaka a wajen birnin Khan Younis dake kudancin zirin na Gaza.
Jami’an asibitin Nasser dake kusa da wurin sun bayyana a yau Laraba cewa, adadin mutanen da harin ya hallaka ya kai 30, ciki harda yara 8, tare da jikkata fiye da mutum 50.
-AP
Dandalin Mu Tattauna