Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Sha Alwashin Daukar Fansa Kan Kisan Ismail Haniyeh


Shugaban Iran Masoud Pezeshkian lokacin saduwarsu da shugaban kungiyar Falasdinawa
ta Hamas, Ismail Haniyeh, a Tehran, Yuli 30, 2024
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian lokacin saduwarsu da shugaban kungiyar Falasdinawa ta Hamas, Ismail Haniyeh, a Tehran, Yuli 30, 2024

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani a sakon ta’aziyya da ya aika kan kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh, ya bayyana cewa za su dauki fansa kan kisan da aka yi wa Haniyeh.

Ya kuma ce Iran ta na gudanar da bincike amma mutuwarsa za ta kara karfafa dangantaka ne tsakanin Iran da Falasdina.

Palestinians Hamas
Palestinians Hamas

A yau Laraba ne kasar Iran da kungiyar masu fafutak suka sanar da rasuwar shugaban Hamas Ismail Haniyeh, jim kadan bayan halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar,

Haniyeh, wanda ya shugabanci Hamas tun shekarar 2017, ya kasance ya na gudun hijira a Qatar.

Ba a bada cikakkun bayanai game da kisan ba sai dai Hamas ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Iran.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kisan, amma ana zaton Isra’ila, wadda ta sha alwashin kashe Haniyeh da sauran shugabannin Hamas saboda harin da kungiyar ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba wanda kuma ya kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 250.

Hamas dai ta zargi Isra'ila da aikata kisan. Sai dai Isra’ila ba ta mayar da martini game da lamarin ba.

A ranar Talatar ne Isra’ila ta kai wani hari a birnin Beirut, wanda ta ce ya yi sanadin kashe wani babban kwamandan kungiyar Hezbollah da ake zargi da hannu wajen kai hari a karshen mako da ya yi sanadin mutuwar matasa 12 a tsaunukan Golan da ke karkashin ikon Isra’ila.

Kasar Masar ta yi Allawadai da kisan gillar da aka yiwa Shugaban Hamas Isma’il Haniyeh da wani kwamandan kungiyra Hezbollah, inda ta bayyana hakan da mummunan ci gaban daka iya yin barazanar fadadar rikici zuwa sauran sassan gabas ta tsakiya.

Falasdinawa masu zanga-zanga akan kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran, a Hebron
Falasdinawa masu zanga-zanga akan kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran, a Hebron

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar wajen masar tace zafafa hare-haren da Isra’ila ta yi a kwanaki 2 da suka gabata ya sake rikirkita tattaunawar tsagaita wuta a yakin da ake yi tsakanin Isra’ilar da kungiyar Hamas.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG