A firar da Muryar Amurka ta yi da Alhaji Asumana Mahammadou, wani na hannun daman shugaban kasar, Nijar Mahammadou Issoufou, yace matakin da shugaban ya dauka tamkar amsa ce ga korafin mutanen kasar.
Yace dole ne shugaban kasa ya saurari korafin mutane. Rage mashawarta ba wata matsala ba ce domin ba aikin din-din-din su keyi ba.
Mashawartan sun yi na'am da matakin da shugaban kasa ya dauka domin abu ne da 'yan kasar suka nema a yi.
Alhaji Asumana Mahammadou yace rage mashawartan ya yi domin a da sun yi aiki da wasu jam'iyyu da basu san yakamata ba. Amma a wannan sabuwar tafiyar sun samu wadanda suka san abun da su keyi da zasu iya aik tare.
Akan ko wasu cikin wadanda aka sauke zasu fusata, Alhaji Asumana Mahammadou yace basu da hujjar fusata domin an yi tafiyar shekaru biyar da su, yanzu kuma sabuwar tafiya ce. Su mashawartan abubuwan da ake bukata su gabatar a karkara sun gabatar saboda haka aikinsu ya kare.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5