Shugaban Karamar Hukuma a Abuja Ya Ki Mutunta Umarnin Kotu - Talakawa

Kotu

Bayan da wata kotu a Abuja ta ba kwamishinan ‘yan sandan birnin umarnin ya kama shugaban karamar hukumar Gwagwalada a kan kin mutunta hukuncin koto a baya, na kwato wa wasu talakawa hakkokin filinsu da aka kwace ba bisa ka’ida ba, har yanzu ana kai ruwa rana, lamarin da ya sa talakawan suka koka.

A ranar Alhamis din makon jiya ne babbar kotun tarayya da ke da zama a yankin Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta zartar da hukunci tare da ba da umarnin cewa kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja ya kama shugaban karamar hukumar Kuje Alhaji Abdullahi Sabo, bisa kin mutunta umarninta na watan Janairun shekarar 2023, sama da watanni takwas kenan, kamar yadda Barrister Alex Zirra Teru da ya wakilci talakawan a kotu ya bayyana.

Tun bayan zartar da hukuncin na watan Janairu ne gomman talakawan da kotu ta mayar wa filin kasuwancinsu da aka kwace ke dako da zirga-zirgar komawa kan batun filin don ci gaba da kasuwanci a Wowo Park, lamarin da ya gagara ganin yadda wanda aka kai kara ya yi kememe ya ki mutunta umarnin kotun.

Alhaji Sani Imam, mai kamfanin Mardiyya Barbecue kuma daya daga cikin mutanen da aka kwace wa filin a Wowo Park, ya bayyana farin ciki kan umarnin kotu na garkame shugaban karamar hukumar Kuje, yana mai cewa kamata ya yi wannan ya zama izina ga shugabanni masu rike da madafun iko.

Sai dai kamar murna ta fara koma ciki ganin yadda wadanda shugaban karamar hukumar ya bai wa filin da ya kwace ke ci gaba da aiki ba tare da shakkar abin da kotu ta zartar a makon jiya ba, in ji jagoran wadanda aka kwacewa filayen.

A gefe guda, fitaccen masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Barista Mainasa Kogo, ya ce duk wani wanda yake rike da wani mukami na hukuma ya kamata ya zama na farko wanda zai rika girmama doka da oda, yana mai cewa sanyin-sanyin da ake gani a bangaren shari’a ke kawo rashin mutanta doka da gwamnati.

A ranar 4 ga watan Yulin shekarar 2020 ne wasu masu kananan sana’o’in da aka kwace wa filin da suke gudanar da kasuwancinsu na yau da kullum ba bisa ka'ida ba, suka shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke da zama a yankin Kwali na birnin tarayya Abuja, inda suka kwashe sama da watannin 30 suna zirga-zirgar zuwa kotu domin neman a kwato musu hakkokinsu kafin hukuncin watan Janairun 2023 da ya maida musu filin nasu amma kuma har yanzu a ke ci gaba da kai ruwa rana.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Karamar Hukuma a Abuja Ya Ki Mutunta Umarnin Kotu - Talakawa