Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Da Obi Za Su Sake Daukaka Kara A Kotun Koli


Atiku da Obi
Atiku da Obi

‘Yan takarar manyan jam‘iyyun adawa a Najeriya sun ce za su sake daukaka kara kan hukuncin wata kotu da ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabrairu, inda suka yi ikirarin cewa an tafka magudi akwai kuma kura-kurai, in ji lauyoyinsu.

WASHINGTON, D.C. - Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da ya zo na biyu, da kuma dan takarar Labour Party Peter Obi wanda ya zo na uku, sun roki kotun da ta soke zaben, suna zargin cewa komai game da wannan zabe na cike da magudi da kuma gazawar hukumar zabe na tattara sakamakon zaben ta hanyar yanar gizo. Suna so a tunbuke Tinubu.

Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Sai dai kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Laraba ta yi watsi da kararrakin da suka shigar, daya bayan daya a hukuncin da kotun da dauki sama da sa’o’i 11.

Hukuncin ya biyo bayan irin salon da aka yi a shekarun baya a zabukan da suka gabata a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka, inda babu wata shari'ar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ta taba samun nasara tun bayan da Najeriya ta koma kan turbar dimokradiyya a shekarar 1999.

Wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi
Wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi

Lauyan Obi Livy Uzoukwu ya shaidawa manema labarai cewa tawagarsa za ta karanta cikakken hukuncin sannan ta sake daukaka kara a kotun koli.

"Muna da kwakkwaran umarni daga wanda muke karewa na kalubalantar hukuncin ta hanyar sake daukaka kara. Da zarar mun samu hukuncin a hannu za mu ci gaba da aiki," in ji shi.

Abubakar Atiku
Abubakar Atiku

Lauyan Atiku, Chris Uche shi kuma ya ce "ba mu sami adalci ba" kuma za mu sake daukaka kara, ya kara da cewa "gwagwarmayar za ta ci gaba."

Ya kamata a shigar da kara a kotun koli a cikin kwanaki 14 ne daga ranar da kotun ta yanke hukuncin. Sannan kotun kolin tana da kwanaki 60 don sauraron karar, sannan kuma ta yanke hukunci.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG