Shugaban hukumar NMDPRA, Injiniya Faruk Ahmed ya ce tun watan Febrairun shekarar 2022 ne ya kamata gwamnati ta janye tallafin man fetur

Your browser doesn’t support HTML5

Injiniya Faruk Ahmed ya bayyana hakan ne a Wata Hira ta musamman da Muryar Amurka, inda ya yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga farga tare da mika bukatar dilallan man fetur su buda gidajen mai, su rika sayar da man saboda kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi 'yan kasa