Sanarwar da hukumar gidajen yarin Sokoto ta fitar dauke da sa hannun jami'inta mai hulda da jama'a ASP Faruk ta ce wasu tsageru ne dauke da makaman gargajiya suka kaiwa jami'anta hari a lokacin da suke kokarin kai wasu mutane 18 da ake tuhuma zuwa kotu.
Sanarwar ta ce 'yan tsageran sun yi kokarin kubutar da mutanen karfi da yaji. Sanarwar ta ci gaba da cewa jami'an 'yan sanda sun mayar da martani nan take domin taimakawa jami'an gidan yarin inda suka samu nasarar karewa tare da mayar da wadanda ake tuhuma zuwa gidan kaso.
Amma babu inda hukumar ta ambaci mutuwar mutane biyu da aka kashe a lokacin yamutsin duk da cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Muryar Amurka ta tunkari shugaban hukumar gidajen yarin Sokoto Haruna Na Baba. A cewarsa basu da labarin wani harbi balantana mutuwar wasu. Aikinsu shi ne kiyaye wadanda suke gidan kaso.
Amma rundunar 'yansanda da ta lura lamarin na neman komawa kanta ta fito karara ta wanke kanta tare da cewa jami'an gidan yari suka yi harbin da ya kashe mutane biyu.
DSP Cordelia Nwanwe kakakiyar rundunar 'yan sandan ta ce abokan wadanda ake tuhuma suka kaiwa jami'an gidan yarin hari da zummar kubutar da 'yanuwansu da ake tuhuma a lokacin ne wani jami'in gidan yarin ya yi harbi a iska inda harsashi ya sami wasu matasa. An ruga da wasu asibiti amma biyu daga cikinsu sun rasu. Yanzu daya yana jinya.
An tattara harsashen da ka harba yanzu suna hannun 'yansanda domin aiwatar da bincike. An kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
A saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5