An baza jami'an tsaro a wani mataki na shirin ko-ta-kwana a tsakiyar birnin Sokoto, a daidai lokacin da ake zaman dar-dar, biyo bayan harbe wasu matasa biyu da ake zargin wani jami'in hukumar kula da gidajen yari ya yi.
Rahotanni sun ce tuni matasan biyu da aka harba suka rasu, yayin wani matashin daya yake jiyyar raunin da ya samu.
A cewar wasu da suka shaida lamarin wanda ya faru da sanyin safiyar Laraba, lokacin da jami’an hukumar gidajen yari ta Najeriya, suke kokarin kai wani da ake tuhuma a kotun.
Bayanai sun yi nuni da cewa motar da ke dauke da mutumin da ake tuhuma ta lalace, inda aka yi kokarin sauya mai mota.
Wasu majiyoyi da ba a tabbatar ba sun ce wasu magoya bayan wanda ake tuhuma din sun yi amfani da wannan dana suka yi yunkurin kubutar da shi.
Hakan ya sa daya daga cikin jami'an gidan yari da ke kula da mutumin ya bude wuta.
Muryar Amurka ta tuntubi kakakin rundunar hukumar gidajen yari ta Najeriya shiyyar Sokoto, amma ya ce sai nan gaba kadan za su yi magana domin yanzu haka suna gudanar da bincike kan lamarin.
Amma rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar wannan lamari.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Murtala Faruk Sanyinnan:
Facebook Forum