Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Damke Wasu Cikin Wadanda Suka Kai Harin Zamfara


'Yan sanda a Minna su na nuna makaman da suka kwace daga hannun 'yan daba
'Yan sanda a Minna su na nuna makaman da suka kwace daga hannun 'yan daba

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwa cikin daren nan cewa ta kama manyan shugabannin da suka kitsa kai mummunan harin da ya hallaka mutane fiye da arba'in a Jihar Zamfara

Hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwa cikin daren nan cewa ta damke manyan wadanda ake zargi da kitsawa da kuma kai mummunan harin da ya hallaka mutane fiye da arba'in a yankin karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara a makon da ya shige.

Wadanda 'yan sandan suka ce sun kama kuwa sune Halilu Garba wanda aka fi sani da suna Mabushi mai shekaru 45 da haihuwa; da Zubairu Marafa da ake kira Wakili dan shekaru 45 da haihuwa shi ma; sai kuam Nafi'u Badamasi wanda ake kira Zakiru, mai shekaru 40.

Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CSP Moshood Jimoh, ya bayar ta ce mutanen da aka kama din su na bayar da muhimman bayanai dake taimakawa a ci gaba da binciken da ake yi kan yadda aka kulla da kuma kai wannan mummunan hari a Zamfara.

Kama wadannan mutane uku da aka yi, yazo kwana guda a bayan da babban sufeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ziyarci Jihar ta Zamfara.

Ga karin bayani a rahoton Hassan Maina Kaina

'Yan Sanda Sun Ce Sun Kama Jigogin Harin Zamfara - 0'52"
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:52 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG