Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Tura Ministan Tsaro Zuwa Zamfara


Janara Mansur Dan Ali Ministan Tsaro
Janara Mansur Dan Ali Ministan Tsaro

Wannan matakin ya biyo bayan kashe wasu 'yan kasuwa fiyeda 40 a yankin Zurmi na Zamafara.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura ministan tsaro Najeriya Birgediya Janar Mansur Dan Ali, zuwa Zamfara, jahar da shi Ministan ya fito, bayan da barayi suka kashe wasu 'yan kasuwa a yankin Zurmi na jahar cikin makon nan.

Ana sa ran ministan ya tattara bayanai ya hada rahoto ga shugaban kasa kan matsalar tsaro a jahar, wadda bisa alamu yaki ci yaki cinyewa.

Gwamnan jahar Abdulaziz Yari, ya jagoranci tawagar Gwamnoni biyar suka ziyarci yankin da lamarin ya faru.

Gwamna Yari yayi kira ga jami'an tsaro su dauki kwararan matakai na shawo kan matsalar tsaro da jahar take fama dashi.

Ga karin bayani daga Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG