Shugaban CAN ba Shike Amfani da Jirgin Samansa a Lokacin da Aka Kama Shi Dauke da Kusan Dala Miliyan 10 a Afirka ta Kudu ba

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci hedkwatar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya dake Abuja, mataimakin shugaban kungiyar mai kula da jihohin arewa maso gabas.

Majami'ar Word Of Life Bible Church ta shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, Pasto Ayo Oritsejafor, ta ce jirgin saman da hukumomin Afirka ta Kudu suka kama dauke da tsabar kudi Dala miliyan 9 da dubu 300, mallakin shugaban nata ne, amma kuma ya riga ya bayar da hayarta tun watan da ya shige.

Majami'ar ta ce ba ya da masaniya game da abinda jirgin yake yi a Afirka ta Kudu ko kuma abinda ya ke dauke da shi.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci hedkwatar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya dake Abuja, mataimakin shugaban kungiyar mai kula da jihohin arewa maso gabas, Rev. Shu'aibu Bel, yayi masa bayanin cewa shi ma kamfanin da Pasto Oritsejafor ya ba hayar jirgin ya sake bayar da shi ga wani, kuma abu ne da aka saba yi a harkar zirga zirgar jiragen sama.

Yace jami'an tsaron Najeriya ne suka dauki hayar jirgin domin sayo makaman da zasu yi amfani da su domin tsare mutuncin kasa.

Amma kuma wani masanin harkar tsaro a Najeriya, Manjo Yahaya Shunku mai ritaya, yace wannan wani sabon kauli ne a ce za a dauki tsabar kudi mai yawa haka domin zuwa sayen makamai. Yace akwai mamaki a ce jami'an tsaron gwamnatin kasa zasu dauki tsabar kudi su kuma shiga jirgin wani farar hula zuwa wata kasa domin sayo makamai.