Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari a Makarantar Horar da Malamai ta Kano


Hoton fashe-fashen boma-boman da suka faru a Kano.
Hoton fashe-fashen boma-boman da suka faru a Kano.

Biyu daga cikin'yan bindigan da suka kai hari sun mutu.

A cigaba da rahoton tashin wasu bama-bamai da suka faru a makarantar horar da malamai da ake kira FCE a Kano, VOA ya zanta da wani malami wanda yace “yaji tashin bindiga da fashewar Bam, ganin mutane na gudu yasa shima bai yi wata-wata ba sai ya daga da gudu. Gab da tsallake wata Katanga, bam na biyu ya tashi. A ta bakin malamin wanda ba a fadi sunansa ba, yace akalla yaga gawarwakin mutane kusan goma.

Haka wani dake cikin masu ceton rai da ba a fadi sunan sa ba yace, mutum biyu cikin wadanda abin ya shafa na cikin ‘yan bindigar.

Wakiliyar muryar amurka Baraka Bashir, ta sami zantawa da Asp Magaji Musa Majiya, wanda ya tabbatar da cewa jimlar mutanen da suka rasa rayukansu sha-ukku ne, mutane talatin da hudu kuma sun jikkata. Ya kara da cewa biyu daga cikin wadanda suka kai harin sun mutu, Kuma an iya samun bindigoginsu guda biyu.

Rahoto daga Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG