Modu Sheriff yace ya zo ne ya basu hakuri. Yace masifa ce Allah ya kawo masu.
Ya kira mutanen Borno da cewa su taru su roki Allah. Gwaji ne Allah ya yiwa jihar. Kuma duk abun da ya zo daga Allah kaddara ce daga gareshi. Duk abun da ya san zai kawo sauki zasu yi.
Akan zargin da Stephen Davies wani dan kasar Australia yayi inda yace Modu Sheriff na cikin wadanda suka dauki nayin 'yan kungiyar Boko Haram sai yace duk maganar kame kame ce. Davies yace yayi magana da 'yan jarida tun daga Australia. A can ma bai yi magana da gidan talibijan kasar ba. Bai yi da na Ingila ba. Bai fadawa jami'an tsaron Borno ko na tarayya ba. Don haka idan yana da gaskiya kamata yayi ya fito fili da kwararan shaidu.
Modu Sheriff ya hakikance shiri ne na wadansu daga Najeriya domin su lalata sunansa a wurin mutane. Amma Allah Ya fisu. Shin shi baturen a ina ya ga Boko Haram har suka fada mashi shi ne mai daukar naiyinsu.
Idan gaskiya shi ne yake basu kudi ai zasu boye sunansa. Yace sun samu labarin yadda aka kawoshi Maiduguri. Daga Kano aka daukoshi aka kaishi Maiduguri. Yace amma ba da dadewa ba gaskiyar zata fito.
Babu wani dan jihar Borno da bala'in bai shafa ba. Yace shi kansa danuwansa uwarsu daya ubansu daya 'yan Boko Haram suka fara kashewa. Sun kashe shugaban jam'iyyarsa. Sun kashe wani danuwansa. Duk mutane Borno sun sani. Idan shi ne yake basu kudi shi ne kuma zasu so su kashe.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.