Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyar Adawa na Sukar Rundunar ‘Yansanda Mai sa Ido a Lamuran Zabe


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega yana nuna jadawalin zaben shekara ta 2011 (File Photo).
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega yana nuna jadawalin zaben shekara ta 2011 (File Photo).

Ana takura ma 'yan jamiyar adawa akan batun kamfe

Mukaddashin Speta-Janar din hukumar ‘yan sanda Mallam Suleiman Abba, ya kirkiro wani sashi a rundunar da zai duba da bada shawarwari akan harkokin zabe. yin hakan bai rasa nasaba da yawaitar korafin saba dokar zabe, wajen fara kamfe din zabe gabanin lokacin da aka tsara.

Rundunar dai na samun suka daga jam’iyyun ‘yan adawa na takura masu in sun aikata wani lamari mai kama da kamfe da ake yi, amma hakan tamkar bai shafar jam’iyya mai mulki. Sanata Danjuma Goje na daya daga cikin wadanda suka yi korafin cewa ‘yan sanda sun takura masu biyo bayan shiga mazabar sa da yayi a jihar gombe.

A wata hira da wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya yayi da Sanata Goje, ya bayyana cewa laifin da aka zarge shi dashi shine na shiga jihar da dunbin jama’a ba lokacin zabe ba.

Sanatan ya kara da cewa tarurrukan da jam’yar PDP ke yi, wanda a kwanan nan ma rumfa ta ta ruguje da gwamna da sauran ‘yan jam’iyar a Minna, ba a ce komai ba. Haka kuma cikin makon nan ma za a yi taron ‘yan jam’iyyar PDP a jihohin arewa maso gashin Najeriya a jihar Gombe.

Shi kuma farfesa Attahiru Jega da aka tuntube shi akan batun yace “manna hoto da yin kirari bai saba ma doka ba amma kyakkyawar mu’amala da jami’an tsaro na da muhimmanci sosai.” Ya kara da cewa, jami’an su kanyi kididdiga su ga inda ake tunani samun matsala da kuma matakan da ya kamata a dauka.

Za a yi zaben na shekarar 2015 a watan Fabairu, a hukumnace kuma za a fara yin kamfe ne a watan nuwambar wannan shekarar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG