Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana kan Neman Jirgin Saman Sojan Najeriya


Jirgin Saman Yakin Najeriya Kirar Alpha-Jet irin wanda ya bace a Adamawa.
Jirgin Saman Yakin Najeriya Kirar Alpha-Jet irin wanda ya bace a Adamawa.

An sami rahotanni masu karo da juna akan inda jirgin saman sojan Najeriya yake.

Kwanaki shidda bayan bacewar jirgin saman Najeriya mai sauna Alpha jet wanda kawo yanzu ma ba a san inda jirgin ya shiga ba, an sami rahotanni masu karo da juna akan inda jirgin yake.wasu manoma sunce jirgin ya fadi ne a yankin Gabun a karamar hukumar Gambi, wasu kuma sun ce jirgin yaci karo ne da fushin ‘yan kungiyar Boko Haram yayin da suka kai wani farmaki a garin Michika inda yanzu haka ma yake hannun ‘yan kungiyar.

Yayinda wadannan bayannan ke fitowa, babban Hafsan askarawan sojan saman kasar Adesola Omosun, a wata hira da yayi da wasu kafafen yada labarai akan halin da ake ciki, yace har yanzu dai babu wani labarin inda jirgin yake, duk da dai ya yaba ma jama’a akan irin bayanan da suke badawa,

Haka ita ma gwamnatinm jihar ta Adamawa, ta nuna kaduwar ta akan bacewar jirgin a wata sanarwa da ta fidda. Sakataren yada labaran Mukaddashin gwamnan jihar Mr. Solomon Kumanga, ya bayyana yadda gwamnatin jihar tayi juyayi sosai akan hasarar da aka yi, musamman na matukan jirgin da a halin yanzu ba a san inda suke ba. Mr. Solomon ya kara da cewa jirgin yana taimaka wa wajen yaki da ‘yan Boko Haram

Kawo yanzu dai, jiragen sama masu saukar ungulu ne ke ta shawagi a yankin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG