Yau Talata shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania zasu ziyarci birnin Pittsburg, kwanaki uku bayan da wani ‘dan bindiga ya bude wuta a wani wajen ibada a birnin.
WASHINGTON DC —
Trump da jami’an gwamnatinsa sun zargi kafafen labarai da yada kiyayya wadda ta yi sanadiyar kai harin, tare da aika ababen fashewa ga manyan ‘yan siyasa masu sukar lamirin shguaban kasa.
Abokan hamayyar Trump na siyasa sun zarge shi da raba kawunan Amurkawa, saboda irin kalaman da yake yawan yi kan ‘yan jam’iyyar adawa ta Democrats, da ma duk wadanda suka nuna rashin amincewa da yadda yake gudanar da mulki.
Trump ya bayyana mummunan harin da aka kai ranar Asabar a birnin Pittsburgh da ya kashe masu bauta mutum 11, ya kuma raunata wasu shida. Ya ce wannan mummunan harin kiyayya hari ne akan duk bil Adama. Dole ne sai an yi aiki tare domin fitar da irin wannan kiyayya daga duniyar nan.