Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mutum Ya Kashe Yahudawa 11 a Amurka


Wasu Yahudawa a harabar masujjadarsu
Wasu Yahudawa a harabar masujjadarsu

A wani mummunan al'amari na nuna kiyayya ga al'ummar Yahudawa, wani bature dan akidar kyamar wasu jinsuna, mai su na Roberts Bowsers, ya hallaka yahudawa 11 a wata masujjadarsu a Amurka.

Wani mutun ya yi ta daga murya ya na cewa, "dole kowane ba-Yahude ya mutu," ya kutsa cikin wata masujjadar Yahudawa a Pittsburg yayin da ake sujjadar Asabar, ya yi ta harbin kai mai uwa da wabi, ya kashe mutane 11, wanda shi ne na baya-bayan nan a harbe-harben mutane da yawa da akan yi a Amurka.

Mutane shida, ciki har da wani jami'in 'yan sanda wanda ya tinkari maharin, sun ji raunuka, a cewar jami'ai, wadanda su ka ce biyu daga cikin farar hulan da ke cikin wadanda su ka ji raunukan na cikin mawuyacin hali.

Wannan, "da alamar shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa ma al'ummar Yahudawa a tarihin Amurka," a cewar kungiyar da ke yaki da al'adar tsana ta Anti-Defamation League.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta bayar da umurnin a saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda a duk gine-ginen gwamnati har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba don nuna alhalin wadanda wannan mummunan abin tashin hankalin ya rutsa da su.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG