Dubi ra’ayoyi
Print
An shiga amfani da alamar tauraron Dauda don nuna alhinin kisan Yahudawa a Pittsburgh, jahar Pennsylvania ta Amurka.
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.
A birnin Jos da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, farashin gawayi na girki ya kusan rubanyawa a 'yan makonnin nan, yayin da mutane suka koma amfani dashi saboda tsadar gas na girki da kuma rashin wutar lantarki.Wannan ya haifar da damuwa daga masu fafutukar kare muhalli da kuma masana kiwon lafiya
A kasashen yammacin Afirka, musamman Ghana da Najeriya, ana samun karuwar cibiyoyin koyawa matasa damfara ta intanet, wadanda ake kira "hustle kingdoms" a turance. Timothy Obiezu ya ziyarci daya daga cikin wadannan cibiyoyin kuma ya hada wannan rahoto daga Legas.
Kasar Qatar ta dakatar da tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas saboda abin da ta kira, rashin mayar da hankali daga bangarorin da ke fada da juna. A halin da ake ciki kuma, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankunan Gaza a kan Hamas da Hezbollah dake Lebanon.
Har haryanzu kasashen Afrika na ci gaba da bayyana ra’ayoyi da suka sha banban dangane da nasarar Donald Trump ta komawa fadar White House. Wasu na jin dadi da shaukin ganin abin da zai biyo baya, wasu kuma na tunawa da mulkin shi na farko.
A lokacin yakin neman zaben shi, Donald Trump ya yi alkawarin aiwatar da manyan abubuwa da suka hada da tsaron kan iyaka da karfafa tattalin arziki. Alkawuran na sa dai suna da girma, to amma ba a babu cikakkun bayanai kan yadda Trump din zai aiwatar da wadannan manufofi. Ga rohoton Tina Trinh.
Facebook Forum