Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sayoc Da Ya Aikewa Obama Bam Zai Bayyana Gaban Kotu Gobe Litinin


Cesar Sayoc
Cesar Sayoc

Ana sa ran mutumin nan da aka kama kuma aka caje shi a ranar Juma’a da aika da akalla kunshi 13 dauke da abubuwar fashewa zuwa ga masu sukar lamirin shugaban Amurka Donald Trump, zai fara bayyana a gaban kotu, a cewar wasu rahotanni daga jami’an tsaro.

Wata majiyar hukumar tsaron ta fadawa labaran CBS cewa Cesar Sayoc dan shekaru 56, wanda ke zama a Aventura a jiahar Florida, zai bayyana gaban kuto a ranar Litinin, yayin da CBS din tace Sayoc zai gurfana ne a gaban alkalin tarayya a birnin Miami na Florida a gobe Litinin.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya buga bayanin da wani jamai’in hukumar tsaron ya yi, yana cewa da farko Sayoc zai fara bayyana ne gaban kotun Florida kafin ya je ya huskancin caje cajensa a kotun tarayya a New York, inda aka samu biyar a cikin abubuwar fashewa 12. Jami’an hukumar tsaron basu da izinin yin bayani a kan shari’ar, lamarin da yasa aka sakaya sunayensu.

Sayoc tsohon mai laifi, yana husnkantar caje caje guda biyar ne a kan shirya makircin aikewa da bama-bamai na tsawon mako guda.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG