A jiya Litini Trump ya bayyana shirinsa na yin jawabi ga kasa ta gidan talabijin, jim kadan bayan da Sakatariyar Yada Labaran Fadar White House Sarah Sanders ta ce shugaban na Amurka zai gana da dogarawan tsaron kan iyaka mai tsawon kilomita 3,200 tsakanin Amurka da Mexico. Ta ce za a ji karin bayani nan gaba kadan akan tafiyar ta sa.
Ziyarar ta Trump zuwa kan iyakar ta zo ne a daidai lokacin da aka shiga kwana na 17 a jere da rufe wasu ma’aikatun gwamnatin tarayyar Amurka, sanadiyar takaddamar da ake yi kan bukatarsa ta a samar da dala biliyan 5 don gina shingen da zai hana bakin haure kwararowa, akasari daga kasashen yankin tsakiyar nahiyar Amurka.
Amma jam’iyyar adawa ta Democrat taki amincewa da dala biliyan 5 da ya nema na gina Katanga, sai dai tayi masa tayin dala bilyan 1.3 a cikin sabon kasafin kudaden da za a kashe kan tsaron kan iyaka.