Shugaba Obama Ya Zanta Da Amurkawa Akan Bambancin Launin Fata Da Cudanyar Jinsuna

Shugaban Amurka Barack Obama ya kwashe kwanaki biyu a jere, yana wata doguwar tattaunawa da Amurkawa kan batun cudanyar jinsina da kuma yadda 'yan sanda ke ma al'ummomi tsiraru.

Wannan taron ganawa da jama'a, wanda ba a saba yi ba, an gudanar da shi ma da yammacin jiya Alhamis a birnin Washington DC, sannan aka yada shi da daren jiya Alhamis din a gidan talabijin na ABC da wasu kafofi masu dangantaka ta ABC din a Amurka, wanda aka kuma yada a fadin duniya ta BBC.

Obama ne Shugaban kasar Bakar fata na farko., to amma yayin da ya ke dosar karshen zamansa a Fadar White House na tsawon shekaru 8, wani binciken da kafafen labaran CBS da New York Times ya nuna cewa sulusi biyu na Amurkawa na ganin babu dangantaka mai kyau tsakanin jinsina daban-daban na kasar kuma rashin jituwar mabanbantan harsuna ya wuce misali a yanzu.

Obama ya gana ranar Laraba na tsawon sa'o'i hudu a Fadar White House da manyan jami'an tsaro da kuma manyan shugabannin Bakar fata, to amma ya ce har yanzu Amurka ba ta yi kusa waraka daga rashin yaddar da aka kwashe shekaru gommai ana izawa tsakanin bangarorin biyu ba.