"Babu abin da zai sa mu daina yaki da ta'addanci," a cewar Hollande, a jawabinsa ga kasar da asubahin jiya Jumma'a. Ya yi nuni da harin da aka kai birnin Paris a watan Oktoban da ya gabata, ya na mai cewa daukacin Faransa na fuskantar barazanar ISIS. "Kasar Faransa gaba dayanta na fuskantar barazanar ta'addanci. Dole ne mu yi matukar taka tsantsan mu kuma nuna jajircewa."
Maharin, wanda shi ma ya mutu, wanda aka ce dan asalin kasar Tunisiya ne mai shekaru 31 da haihuwa, wanda ya zauna a garin na Nice, ba a tabbatar da alakarsa da ISIS ba. Shugaba Hollande ya ce hukumomi za su cigaba da binciken yayanin maharin.
Hollande ya ce dokar ta-bakin da aka kafa a Faransa a baya, wadda da za ta kare a wannan wata, za a tsawaita ta zuwa karin watanni uku, kuma za a kara yawan sojoji da 10,000 a fadin kasar. Ya ce kasar Faransa za ta jaddada rawar da ta ke takawa a Siriya da Iraki.
Maharin ya sheko ne a guje da babbar motar daukar kaya, ya karkatar da ita, ya yi kan cincirindon mutane a birnin Nice da daren jiya Alhamis, a wurin da ake bukukuwan ranar ta Bastille, wadda rana ce ta zagayowar 'yancin kan Faransa.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan Faransa ta ce adadin wadanda su ka mutu din ya kai 80, sannan, a ta bakinta, an "gama" da maharin. Daga bisani jami'an tsaro sun gano cewa motar na dauke da bama-bamai, da gurnet-gurnet da sauran makamai.
Nice, wanda shi ne birni na biyar a girma a kasar ta Faransa, wanda shi kuma ne babban birnin yankin Cote d'Azur, ya kasance cikin shirin ko-ta-kwana na jami'an tsaro saboda ko a kara fuskantar wani harin kuma.