A yammacin jiya Laraba, shugaba Obama yayi wani zaman tattaunawa ta tsawon awanni Hudu a fadar White House, da shugabannin ‘yan sanda da gwamnoni da wasu magadan gari da kuma ministar shari’a ta Amurka Loretta Lynch, da wasu wakilan kungiyar fafutukar kare rayukan bakar fata da ake kira Black Lives Matter da turanci.
Tattaunawar dai ta biyo bayan tashin hankalin da ya faru a makon da ya gabata, ciki harda kwantan ‘baunan da ya kashe ‘yan sanda biyar fararen fata a garin Dallas na jihar Texas, wanda wani dan kishin bakar fata yayi bayan da ya fusata da kashe wasu bakaken fata biyu da wasu ‘yan sanda sukayi a Minnesota da Louisiana.
Obama yace kokarin da ake na kawo karshen wannan lamari ba zai yi tasiri lokaci ‘daya ba, saboda ya samo asaline shekaru aru aru.
yace, 'yan sandan 'kasar na jin suna tsaka mai wuya, kuma ana zarginsu ba bisa ka'ida ba cewa suna auna matasa bakaken fata, yayinda al'umomi marasa rinjaye ke ganin shugabanni suna sanyin jiki wajen daukar matakai da suka zama wajibi kan wannan batu.