Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Ta Hana Shugaban Kafofin Yada Labaran Amurka Shiga Kasar


A jiya ne Rasha ta hana shugaban majalisar gudanarwar kofofin yada labaran Amurka, Jeff Shell, shiga kasar.

Majalisar ce Muryar Amurka ke karkashinta kuma bayan da aka hanashi shiga kuma an tsareshi ana masa tambayoyi na tsawon wasu sa'o'i.

Jeff Shell shine kuma shugaban kafar watsa labarai ta NBC. Kamfanin dillancin labaran Rasha ya fitar da rahotan dake cewa, jami’an Rasha sun saka sunan Shell cikin jerin sunayen mutanen da aka haramtawa shiga kasar Rasha, saboda rawar da yake takawa ta yada farfagandaganda kan Rasha.

Jami’an Rasha sun fitar da Shell daga kan layi na masu shigowa a filin saukar jiragen sama a yammacin Talata, duk da kuwa yana rike da visar shiga kasar.

Shell yace an rufeshi a daki na tsawon sa'o'i kafin jami’an su sakeshi cikin jirgin da zai tafi Amsterdam. Shugaban ya fadawa abokin aikinsa cewa an fada masa cewa an haramta masa shiga kasar Rasha har abada.

Ministan harkokin wajen Rasha yace an hana Shell shiga Rasha ne saboda shine shugaban ma’aikatar yada propagandar Amurka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG