Abin mamaki a zabin nata shine, ta nada tsohon magajin gari na London Boris Johnson, a matsayin sakataren harkokin waje. Johnson yana daga cikin jagororin kamfen na neman Birtaniya ta fice daga kungiyar tarayyar Turai. Ya fusata mutanen da suka zabi Birtaniya ta kasance da Kungiyar EU, dama sauran shugabannin Turan da sukayi imanin Birtaniya ta yi gagarumin kuskure.
Haka kuma May ta nada wasu masu goyon Bayan ficewar Birtaniyar kan wasu manyan mukamai, ciki harda tsohon sakataren harkokin waje Phillip Hammond, a matsayin Ministan Kudi da Amber Rudd a matsayin sakatariyar harkokin gida, wato tsohon mukamin da May ta rike.
Dan majalisa na jam’iyar masu ra’ayin rikau ta Conservative David Davis zai rike mukamin sabon ministan da aka kirkira wanda zai jagoranci tattaunawa kan ficewar Birtaniya daga EU. Ana kyautata tsammanin zaman tattaunawar ka iya daukar tsawon shekaru biyu.
May ta zamanto mace ta biyu da zata zama Farai Minista a tarihin Britaniya, bayan marigayiya Margret Thatcher.