Shugaban yace idan da shi baya kaunar arewa da bai sa kudi cikin inganta ilimi a yankin ba ko kuma kafa jami'o'i goma cikin sha hudu da ya kafa, wato ya ba kudu hudu kawai.
Shugaban ya bayyana mamaki yadda ake ta'allaka shugabancinsa da matsalolin da yankin arewan ke fuskanta. Yayi furucin ne a wani gangamin neman sake zabensa da aka soma a Sokoto.
Da ya koma kan tsaro yace ana neman a mayarda lamarin siyasa ne kawai.
Shi ma mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo batun ya tabashi ganin cewa 'yan arewa ne ke rike da mukamai da dama a gwamnatin ta Jonathan. Yace wasu suna cewa gwamnati ce take jawo tashin hankali. Yace don Allah don Annabi wace gwamnati zata sa ana kashe mutanenta. Yace Allah kadai ya san iyakacin muslman dake cikin lamarin.
Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido shugaban yakin neman zaben Jonathan na yankin arewa ya mayarwa gwamnan Sokoto martani har ma da tonon silili. Yace an zabi gwamna Wamako aka so a hanashi shi Lamido ya zo ya shiga tsakani har yanzu yana cewa PDP tana kama karya. Idan kama karya aiki ne to ai an kama an karya domin ya zama gwamna.
Daraktan kemfen din Jonathan Dr Ahamdu Ali da tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa sun yi allawadai da yadda ake ta'allaka siyasar yanzu da addini, musamman a jihar Sokoto.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5