Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashi a Kasuwar Arawa, Jihar Gombe


ana kyautata zaton mutane da yawa sun mutu a fashewar bom din da ya faru a kasuwar Arawa a jihar Gombe

Da maraicen nan ne bom ya tashi a unguwar Arawa dake garin Gombe.

Kasa da sa’o’I uku kafin fashewar bom din, aka sami rahoton cewa an kame wata mota dauke da bomabomai har guda biyar a jihar ta Gombe.

Alhaji Garba Tela da Abdulwahab Mohammed wakilin muryar Amurka, sun fadi cewa bom din ya tashi ne a wata kasuwar Mata dake dankare da jama’a, kuma da alama mutane da dama sun mutu.

Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ba ko suka jikkata, haka kuma ba a ji ta bakin jami’an tsaro ba.

A cikin ‘yan kwanakin nan ana yawan samun hare-hare a jihar Gombe kamar a wasu sassan makwabtan jihohinta. Gombe dai jiha ce da ta hada iyaka da jihohin Borno, Adamawa, da Yobe, ana kyuatata zaton cewa cikin mutanen da suka kwararo zuwa jihar, ba za su rasa nasaba da tashin bomaboman ba, inji Abdulwahab Mohammed.

Bom ya Tashi a Kasuwar Arawa Jihar Gombe - 3'40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG