Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram ta Sake Kai Hari a Gombi Jihar Adamawa


'Yan Boko Haram
'Yan Boko Haram

'Yan Boko Haram sun yi kokarin sake kwace garin Gombi dake jihar Adamawa.

Labarai da dumi-duminsu suna cewa har yanzu 'yan kungiyar Boko Haram suna cikin garin Gombi inda suke ta fafatawa da dakarun Najeriya.

'Yan bindigan sun shiga garin ne ta wata barauniyar hanya. Jama'ar garin suna ta jin harbe-harbe lamain da ya sa suka shige jidajensu. Babu adadin wadanda wannan sabon harin ya rutsa dasu.

Hukumomin tsaro basu yi wani karin haske ba. To saidai gwamnatin jihar ta bukaci jama'a su kwantar da hankulansu. Mr. P.P. Elesha kakakin gwamnan jihar yace sakataren gwamnati yayi magana da jami'an tsaro sun kuma bada tabbacin daukan duk matakan da suka dace domin kawo karshen tashin tashinar.

Harin ya zo ne yayin da al'ummar Hong ke korafi akan irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu ciki sabili da haka suka bukaci a kai masu tallafi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG