Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Shugaba Jonathan Maiduguri ba ta yi Wani Tasiri ba ga Al'ummar Yankin


Shugaba Jonathan a Maiduguri, Janairu 15, 2015.
Shugaba Jonathan a Maiduguri, Janairu 15, 2015.

Al'ummar yankin Maiduguri da kewaye basu yi murna da zuwan shugaba Jonathan ba sosai.

Jiya Alhamis ne shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kai wata ziyarar bazata a garin Maiduguri dake jihar Borno don jajanta ma al’ummar yankin sakamakon mummunan hari da ‘yan boko haram suka kai kwanan nan a garin Baga dake jihar.

Honarabul Saleh Mohammed Banga, dan majlisa ne mai wakiltar karamar hukumar kwai a jihar Borno, shugaban kwamitin yada labaran jihar kuma. Ya fadi cewa basu zan da zuwan shugaban ba balle su shirya marabtar shi.

An kwashe shekaru kusan biyar ana samun munanan hare-haren ‘yan bindiga a yankin, ciki harda sace daliban makarantar Chibok da aka yi a shekarar da ta gabata amma shugaba Jonathan bai taba jajanta masu ba sai yanzu da duniya ta taso shi gaba, inji Honarabul Saleh.

Ga dukan alamu dai zuwan shugaba Jonathan bai yi wani tasiri ba sosai ga al’ummar jihar Borno, da ma jihohin dake kewaye, don wasu ma na ganin cewa shugaban yazo ne kawai saboda zabe na karatowa.

Zuwan Shugaba Jonathan Bai yi Wani Tasiri ba Sosai ga Al'ummar Jihar Borno - 3'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG