Wanna matsayin da jam'iyyar ta dauka yana kunshe ne a jawabin bayan taro da aka karanta.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima shi ne shugaban taron kuma yayi bayani. Yace sun tattauna akan matakan da zasu dauka su tabbatar sun yi nasara a arewa maso gabas. Sun duba wane mataki zasu dauka akan matsalar tsaro da ta addabi yankin domin cimma burinsu na kawo canji a kasar.
Dangane da zancen zabe yace babu wani taimako da ake yi masu. Hakinsu ne su zaba kuma a zabesu. Wannan yana cikin kundun tsarin mulkin kasar har da ma wasu da Najeriya ta sanya hannu ciki. Yace ba akansu a ka fara ba. An taba kai mutanen Okirika su yi zabe a Fatakwal.
Yanzu suna da 'yan gudun hijira fiye da miliyan daya da dubu dari biyar a cikin garin Maiduguri. Yace sun ba kungiyar kiristoci ta CAN miliyan goma domin akwai kiristoci dake gudun hijira a Kamaru. Yace su kawosu Yola su zasu kaisu Borno daga Yola.
Da yaddar Allah za'a yi zabe, kuma ba wani taimako ba ne hakinsu ne su yi zabe. Muddin su 'yan Najeriya ne dole a yi zabe a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
'Dan kwamitin amintattu na jam'iyyar kuma dan takarar sanata daga jihar Gombe Bayero Nafada yayi bayani da cewa suna da kalubalen tsaro a yankinsu. Sun tattauna akai domin ana magana kamar wasu ba zasu yi zabe ba.Kundun tsarin mulkin Najeriya ya sa dole ne a yi zaben.
Alhaji Kanika Mai Lantarki dan majalisar wakilan tarayya ya nesanta kansa daga zargin da wasu suke yi cewa yana da hannu akan canza shekar da wasu 'yan jam'iyyar keyi zuwa PDP a jihar Gombe.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.