Yau Alhamis ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump, zai rattaba hannu akan wani sabon tsarin ciniki da zai auna kasar China, wanda kuma ake jin zai takalo mummunar jayayya a fagen saye da sayarwa a tsakanin kasashen biyu.
WASHINGTON D.C —
Rahottani sun ce Amurka na daukar wannan matakin ne a matsayin martini ga yawan satar fasahun masana’antun Amurka da China ke yi, tana hannuntawa nata kamfanonin.
Ma’aikatar ciniki ta kasar China ta ce tana adawa da kudurin Amurka na daukar wannan matakin ita kadai, na chanza tsare-tsaren ciniki a tsakanin kasashen biyu, ta kara da cewa tana fatar kasashen biyu zasu zauna su maganta don neman mafitar da zata yi wa kowannensu daidai