Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Taya Shugaba Putin Murna Kan Lashe Zaben Shugaban Kasa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Duk da ja masa da kunne da masu bashi shawara kan harkokin tsaro suka yi, Shugaban Amurka Donald Trump ya taya shugaban Rasha murna kan lashe zaben shugaban kasarsa karo na hudu

Shugaba Donald Trump na Amurka ya taya takwaran aikin na Rasha murnar nasarar da ya samu na sake zabensa. Mr. Trump ya mika masa sakon tayin murnar a wata tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho jiya Talata, har suka amince zasu gana a wani lokaci nan bada jumawa ba.

"Wata kila zamu gana nan bada jumawa ba, domin mu tattauna kan batun makamai, mu tattauna kan gasar tara makamai." Shugaban na Amurka ya gayawa manema labarai kamin ya gana da Yerima mai jiran gado na saudiyya Mohammed bin Salman.

Mr. Trump ya ce gasar kera makaman "yana so ya wuce makadi da rawa," amma Amurka, ba zata kyale wata kasa ta mallaki ko kusa da abunda Amurka ta mallaka ba." Cikin wasu batutuwa da shugabannin biyu zasu tattauna akan su sun hada da batun Ukraine, da Syria, da Koriya ta Arewa, inji shugaban na Amurka.

A tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho, shugaba Trump ya jaddada muhimmancin kawar da makaman Nukiliya a zirin Koriya.

Wata sanarwa daga fadar Kremlin, a jiya talata, ta ce,shugaba Trump, da Putin sun yi magana kan muhimmancin aiki tare a kasa-da kasa domin yaki da ta'addanci,takaita yaduwar makaman kare dangi, da kuma hada kai ta fuskar tattalin arziki.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG