Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Tattaunawa Da Kasashen Turai Akan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Brian Hook mai bada shawara akanmanufofin gwamnati a ma'aikatar harkokin wajen Amurka
Brian Hook mai bada shawara akanmanufofin gwamnati a ma'aikatar harkokin wajen Amurka

Yayinda lokacin sabunta yarjejeniyar nukiliyar din Iran ke karatowa Amurka na tattaunawa da kasashen turai da zummar kawo wasu canje canje abun da kuma ita Iran ta ce ba zata amince dashi ba

Amurka ta ce ta yi tattaunawa mai ma ana tsakanin ta da kawayen ta a Turai a cikin satin da ya gabata, akan wasu sauye-sauye game da yarjejeniyar da aka kulla kan shirin Nukilyar Iran, sai dai ta ce tana gudanar da wani shirin na bacin rana, idan shawarwarinsuka sukurkuce, kuma shugaba Donald Trump ya yanke shawara na janye Amurka daga cikin yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015.

Babban jami’in dake kan gaba a wannan tattaunawar daga ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Brian Hook, wanda shine Darektan shirya-tsare tsare kan manufofi, ya shaidawa manema labarai jiya Laraba cewa ba zai iya hasashen ko tattaunawa da Amurka da Birtaniya, da Faransa, da Jamus, na cimma wata yarjejeniya da za ta tallafawa ta farko, domin magance abunda shugaba Trump yake kallo a zaman rauni kan daidaituwar ta farko, za'a iya samun haka gabannin kamin nan da watan Mayu.

Ranar 12 ga watan Mayu ne dai aka tsayar cewa gwamnatin ta Amurka zata yanke shawarar ko ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta wajen sassautawa Iran takunkumin karya tattalin arziki, kamar yadda aka amince tsakanin maynayn kasashen duniyar da Iran.

Iran tace ba zata amince da wani canji a yarjejeniyar ta farko ba, amma kuma jami’an diflomasiyyar kasashen turai sun nuna cewa zasu goyi bayan wasu canje-canje domin ganin an cimma nasara akan wannan yarjejeniyar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG