Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kalubali China Akan Kasuwanci


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Kasashe da dama suna kuka akan yadda China ke karya wasu ka'idojonkasuwanci duk da cewa ta shiga kungiyar kasuwanci ta duniya a shekarar 2001

Daga yanzu zuwa ko wane lokaci ana sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai kalubalanci China kai tsaye, wanda ba mamaki ya rikide ya zamo babban sabani ta fuskar kasuwanci a tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Daukar matakin kan China gameda cinikayya, martini ne kan satar fasaha da daukar wasu fasahohin Amurka zuwa ga wasu kanfanonin China, ana sa ran shugaban na Amurka ya bayyana wadannan matakai awani lokaci yau Alhamis.

A jajibirin da ake sa ran daukar wannan matakan, Jami'ai nan Amurka sun shaidawa manema labarai cewa an kwashe tsawon wata daya ana bincike, kuma ana wannan binciken ne karkashin sashi na 301 na dokar cinikayya ta Amurka ta 1974, gameda take-taken China ta fuskar kasuwanci.

Dama dai da yawan kasashen duniya suna kallon kasar ta China a matsayin wadda ta karya dokokin kasuwancin kasa-da-kasa, duk ko da yake ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya a shekarar 2001.

Hukumomin kasa da kasa sun juma suna kallon China a zaman kasa wacce take saba dukkan ka'idojin cinikayya tsakanin kasashen duniya, duk da cewa ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya a shekara ta 2001.

Sai dai yayin da ake jiran wannan tsattsauran matakin daga Amurka, mahukuntar kasar ta China sun ce sun san cewa wannan lamari zai iya musu illa.

Ahalind a ake ciki kuma, Amurka da tarayyar turai sun shirya tsaf domin fara wani zagaye na shawarwari da zummar warware dukkan wani sabanin ta fuskar kasuwanci, ciki harda daftarin sabon haraji kan karafa da dalma da Amurka take shirin azawa kan kayayyakin da ake shigo dasu kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG