A ranar litinin 11 ga watan Disambar 2023 ne shugaba Ahmed Bola Tinubu na Najeriya, ya kai ziyara birnin Maiduguri dake jihar Borno a Najeriya.
karo na farko kenan da shugaban ya kai ziyara jihar dake arewa maso gabashin Najeriya, tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan mayu.
Gwamnan jihar Borno, Baba Gana Umara Zulum, shi ne ya tarbi shugaban da tawagar shi ,inda daga nan ya jagorance su zuwa fadar mai martaba shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai El-kanemi.
A yayin ziyarar ta sa, shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da wasu motocin sufuri da gwamnatin jihar Borno ta samar domin sauwaka ma al’ummar jihar zirga zirga.
Motocin sun hada da guda bakwai masu amfani da lantarki da iskar gas, da kuma coaster Bus guda talatin da biyar, da kuma wasu dogayen motocin da ake kira coaster masu amfani da gas guda talatin, da ma karin wasu motocin bus din da dama.
Shugaba Tinubu ya kuma jagoranci bude taron shekara shekara na hafsoshin soji a barikin Maimalari da ke garin na Maiduguri. A jawabin shi a gurin taron, shugaba Tinubu ya bayyana taron a matsayin wata shimfida da tunani mai kyau, da za ta samar da yanayin horo mai inganci da zai inganta ayyukan jami’an, yadda za su ci gaba da gudanar da aiyukan kare kasa daga ko wacce irin barazana.
Ya kara da cewa, kalubalen da ake fuskan ta, kalubale ne da ake fuskan ta baki daya, kuma kalubale ne da ba zai mikawa kai bori ya hau ba, a matsayinsa na babban kwamandan askarawan Najeriya.
Da yake tsokaci akan kuskuren da ya kai ga kisan farar hula masu yawa a jihar Kaduna, shugaba Tinubu ya bayyana takaici da bakin cikin faruwar lamarin, ya ce musamman yadda aka rasa rayukan mata da kananan yara wannan lamari da ya kasance abin damuwa matuka, musamman a matsayin mu na wadanda alhakin kare rayukan jama’a ya rataya a wuyan su. Lallai sai an binciki yadda lamarin ya faru, domin kare afkuwan hakan a nan gaba.
A na shi jawabin babban hafsan hafsoshin Najeriya Toufiq Lagbaoja, batun matsalar kalubalen muhalli da ke damun sojojin Najeriya, shine batun da za a maida hankali a kai a nan da shekaru biyar masu zuwa, ya ce a halin yanzu an gudanar da gyare gyare dabam dabam a barikin sojojin dabam dabam a kasar nan.
A karshe shugaban hafsan hafsoshin ya godewa shugaba Tinubu, wanda ya amince da biyan su kudi sama da naira biliyan 18 na hakkokin sojojin da suka kwanta dama a yayin aikin bauta ma kasar su.
Your browser doesn’t support HTML5