Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Kudurin Jagorancin Malaman Afirka A Birnin Fez Na Kasar Maroko


Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI
Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI

Taron kolin na shekara-shekara, karo na 5 na Majalisar Gidauniyar Mohammed na 6 ta Malaman Afirka, ya sami halartar malaman Afirka fiye da 300 daga kasashe 48, ya samar da kudurin da zai zamewa malaman da ke karkashin gidauniyar jagora, wajen tabbatar da manufofin kungiyar a hukumance.

Taron koli na Gidauniyar majalisar Malaman Afirka da Sarkin Maroko, Mohammed na VI ya assasa, ya kumshi mambobin malamai fiye da 300, bayan an sami karin kasashe 14 da suka hada da Burundi, da Cape Verde, da Mauritius da sauransu.

Dokta Ahmed Saeed, babban sakataren malamai na birnin Kumasi ta Ghana, daya daga cikin malaman da suka wakilci Ghana, ya ce Sarkin Maroko, Mohammed na VI ne ya assasa wannan kungiya kuma ya ke daukar nauyinta.

Ya kara da cewa "daga cikin abin da aka tattauna akwai bukatar a ga sauyi a harkokin tafiyar da harkokinmu, ta hanyar komawa ga asali na gargajiya; a samu shugaba daya; kuma idan ya kai ga fatawa, a san wanda zai bayar da amsa, kuma ya dace da abinda Annabi (SAW) ko kur’ani ya nuna."

Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI
Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI

A zaman farko, sakatariyar Gidauniyar ta gabatar da rahoton ayyukan ta na shekarar 2022 da 2023. Sannan ta gabatar da wasu daga cikin ayyukan da za ta gabatar a shekarar 2024 mai zuwa, wanda za'a tattauna a kai kuma a tabbatar da su karkashin kwamitoci hudu; wato kwamitin kimiya da gargajiya; kwamitin Shari’a; kwamitin farfado da addinin Musulunci na asali; da kuma kwamitin sadarwa.

A zaman karshe, wanda aka yi a dakin karatu na masallacin Al-Qarawiyyin mai tarihi da ke garin Faz, an kaddamar da kudurin da zai zamewa malaman da ke karkashin gidauniyar jagorar tabbatar da manufofin kungiyar a hukumance.

Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI
Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI

Babban Limamin masallacin Abuja da ke Najeriya, Farfesa Ibrahim Makari, ya bayyanawa Muryar Amurka mafi muhimmanci daga cikin kudurin.

Ya ce "mafi muhimmancin abin da kudurin ya kunsa shi ne, ya ya malaman Afirka za su ba da gudunmawa cikin tabbatar da zaman lafiya, da kiyaye muhalli, da hadin kan al’umm,; da kore sabani tsakanin al’ummar Musulmi da junansu, da kuma zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi da wadanda ba Musulmi ba."

Farfesa Makari ya kara da cew, maimakon a dinga shigowa da fatawa, to su a matsayinsu na malamai na wannan nahiya ne za su dinga fitowa da fatawar kan abin da ya shafe su.

Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI
Taron Gidauniyar Sarkin Maroko VI

Dokta Nasiba Tahir, malama a jami’ar Islamiya ta Ghana, kuma daya daga cikin mambobin kwamitin kimiyya da al’amuran gargajiya, ta ce a zaman kwamitinsu, sun tattauna yadda Musulman duniya za su hada kai, musamman a inda aka sami dacewa gaba daya. Haka kuma sun mika bukatunsu na yadda za'a taimakawa mata da matasa ta hanyar daukar nauyin ilminsu. Ta ce hakan zai kara musu kwarin gwiwar taimakawa wajen cimma buri.

A gefen taron, an shirya kayataccen bukin bayar da kyautuka ga wadanda suka yi nasara a gasar hardan kur’ani da gidauniyar ta shirya ta yanar gizo a ranar 1 zuwa 3 ga watan Afrilun 2023.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG