Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabi mai sosa zuciya ga al’ummar Amurka a yau Alhamis, inda ya sha alwashin mika mulki ga Donald Trump cikin lumana bayan da babban abokin hamayyar siyasar tasa ya samu gagarumar rinjayen cin zabe a kan Kamala Harris.
Yayin jawabin da ya gabatar a Rose Garden dake fadar White House, ya ce "a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa, zamu mika mulki cikin lumana a Amurka.
"Al'umma ta kada kuri'a ta zabi shugabanninta, kuma sun gudanar da hakan cikin lumana. Muradan al'umma ne zai yi rinjaye. Jiya, na tattauna da zababben shugaban kasa Trump domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zabe.
“Na bashi tabbacin cewa zan umarci ilahirin mutanen dake cikin gwamnatina su yi aiki tare da nasa tawagar domin tabbatar da mika mulki cikin lumana.
Amma Biden, wanda jigo ne a siyasar jam’iyyar Democrat na tsawon shekaru 50, ya koka da abin da ya faru da mataimakiyar shugaban kasa da ya zaba don yin takara tare da shi a 2020 don ta gaje shi.
Ya kuma yaba da tsarin yakin neman zabenta a matsayin abin koyi kuma ya ce ya bata dukkan goyon bayan da ya kamata.