Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Zai Yiwa Amurkawa Jawabi Bayan Nasarar Dawowar Trump


Shugaba Biden ya sha alwashin mika mulki ga Donald Trump cikin lumana bayan da babban abokin hamayyar siyasar tasa ya samu gagarumar rinjayen cin zabe akan Kamala Harris.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden zai gabatar da jawabi mai sosa zuciya ga al’ummar Amurka a yau Alhamis,

Shugaba Biden ya sha alwashin mika mulki ga Donald Trump cikin lumana bayan da babban abokin hamayyar siyasar tasa ya samu gagarumar rinjayen cin zabe akan Kamala Harris.

A wani al’amari da ake ganin zai yiwa Biden daci a rai, zai gabatar da jawabin ne a Rose Garden dake fadar White House a yau da misalin karfe 11 na safiya (karfe 4 agogon GMT) a kan sakamakon zabubbuka da mika mulki ga Trump a wa’adi na 2.

Biden ya janye daga yin takara da Trump a watan Yulin da ya gabata tare da mikawa mataimakiyarsa Kamala Harris tikitin yiwa jam’iyyar Democrat takarar.

Fadar White House ta bayyana cewar Biden ya zanta da Trump a jiya Laraba kuma “ya jaddada aniyar tabbatar da mika mulki cikin lumana tare da karfafa muhimmancin hada kan kasar.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG