NIAMEY, NIGER - Bayan batun ‘yan gudun hijira shugaban zai tattauna da shugabanin al’umma akan matsalolin da ake fama da su a dai lokacin da yankin ke kokarin murmurewa daga tashin hankali da rikicin Boko Haram ya haddasa.
Wannan rangadi dake zuwa a wani lokacin da ake cika shekara guda da kwashe mutanen garin Baroua da na wasu kauyuka da dama daga sansanin da suka shafe shekaru sama da biyar suna hijira sanadiyar tashin hankalin Boko Haram wata dama ce da shugaba Mohamed Bazoum zai yi amfani da ita don bitar yanayin rayuwar al’umomin garuruwan kewayen tafkin Chadi.
Da yake bayyana matsayinsa akan wannan yunkuri Jami’in fafitika na kungiyar AEC Kaka Touda Mamadou Goni na cewa wannan abin a yaba ne.
Banda batun karfafa guiwa ga jami’an tsaro da talakawa, ziyarar ta shugaban kasa a wannan yanki mai samun bakuncin dubun dubatar ‘yan gudun hijirar cikin gida da na waje na hangen tada kungiyoyin agaji daga barci sakamakon lura da yadda tallafin irin wadanan kungiyoyi ya fara karanci.
Makomar matasa wani abu ne da ya kamata a dauka da mahimmanci a wannan lokaci na yaduwar ayyukan ta’addanci da na ‘yan takife musamman a jihar Diffa inda matasa ke korafin rashin morar arzikin man da ake hakowa a yankinsu abinda ya sa Kaka Touda Goni ke hannunka mai sanda.
A nasa ra’ayin wannan rangadi shugaban kasa zai jagoranci taron kwamitin tsaro conseil national de securite haka kuma zai tantauna da shugabanin al’umomin yankin Diffa akan abubuwan da suka fi cinye wa jama’a tuwo a kwarya kafin a makon gobe ya nufi jihar Agadez a ci gaba da ziyarar al’umomin yankunan dake fama da matsalolin tsaro.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5