Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, ya ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar cikin gida da ke wasu kauyukan jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.
Bazoum ya kai ziyarar ce a ranar Juma’a da nufin ba su tabbacin cewa gwamnatinsa ta dauki dukkan matakan da suka dace don mayar da su gidajensu.
Sama da mutane 16,000 ne suka tsere daga matsugunansu a ‘yan watannin nan sakamakon tsanantar matsalolin tsaro a gundumar Torodi da ke jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.
Hakan ya sa Bazoum ya kai ziyara a garuruwan da wadanan mutane suka samu mafaka domin ba su goyon baya a wannan lokaci na tashin hankali, ya kuma fara ne da kauyen Makalondi.
Al’ummar Makalondi da ke karbar bakuncin mutanen kauyuka akalla 10 da suka arce a sanadiyar aika-aikar ‘yan bindiga, sun bayyana farin ciki da wannan ziyara ta Mohamed Bazoum suna masu fatan ganin an gaggauta daukan matakai a wannan yanki da komai ya tsaya cik.
Garin Torodi inda a nan ma mazaunan wasu kauyuka akalla 10 ne suka gudo a farkon watan Mayun da ya gabata, ya sami bakuncin wannan tawaga ta shugaban kasa inda a nan din ma batun tsaro da shirin maida dubban ‘yan gudun hijira garuruwan da suka fito ne aka tantauna akansu .
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan fashin da a can baya suka addabi al’umomin karkarar Torodi na fakewa da aika-aikar ‘yan ta’adda don kara kuntatawa bayin Allah.
Shugaban kasa ya yi kira garesu su tuba su koma kan hanyar gaskiya, ya na mai cewa kofa ta na bude don ba su damar samun canjin rayuwa.