A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin fafitika na kawancen Tournons la Page sun bayyana damuwa a game da yadda hukumomim kasar suka rufe dukkan wata damar gudanar da zanga zanga yayinda yaki da cin hanci da mahandama ya gagari gwamnatin Mohamed Bazoum sai dai wani kusa a jam’iya mai mulki yace babu kamshin gaskiya a wannan zargi.
A rahoton da ta fitar a yau alhamis a gaban manema labarai gamayyar kungiyoyin Tournons La Page tace daga shekarar 2018 kawo yau takardar neman izinin gudanar da zanga zanga a kalla 53 ne hukumomin Nijer suka yi watsi da su yayinda aka kyasta mutane sama da 1000 da aka kulle a kurkuku ba bisa ka’ida ba, lamarin da shugabanin TLP suka ce ya sabawa mulkin Dimokradiya kamar yadda za a ji karin bayani daga jagoransu Maikol Zodi.
Kungiyoyin sun ce sannu hankali hukumomin na Nijer sun fara yunkurin bullo da wani sabon tsarin da za su yi amfani da shi don rufe bakin ‘yan gwagwarmaya.
Yaki da cin hanci da farautar mahandama dukiyar kasa na daga cikin alkawulan da shugaba Mohamed Bazoum ya yiwa ‘yan Nijer a yayin da yake rantsuwar kama aiki sai dai gamayyar Tournons La Page a rahoton da ta fitar tace har yanzu ba ga abin a aikace ba mafarin wannan tunatarwa.
Sai dai kakakin jam’iyar PNDS mai mulki Assoumana Mahamadou ya yi watsi da wannan zargi hasali ma a cewarsa masu wannan ikirari mutane da ke da wata manufa ta boye.
A washegarin darewarsa karagar mulkin Nijer shugaban kasa ya tattauna da kungiyoyin fararen hula inda ya bukaci su taimaka masa wajen yaki da miyagun dabi’un da suka yiwa kasa katutu, lura da yanayin kom gaba kom bayan da ake ciki wajen zartar da wannan kudiri ya sa Tournons La Page ta ruwaito wasu mahimman shawarwari a wani sashe na wannan rahoto a matsayin hanyoyin da zasu taimaka wa shugaba Mohamed Bazoum ya cimma naraorin da ya ce ya na fatan samu a tsawon wa’adin mulkinsa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Soule Moumini Barma: