A Rasha, dubban 'yan kasar ne suka fantsama kan tituna domin zanga zangar nuna rashin amincewa da shirin gwamnati na kara shekarun karbar kudin fansho data bullo dashi cikin watan Yuni, mata daga shekaru 55 zuwa 63, maza kuma daga shekaru 60 zuwa 65. Sun yi zanga zangar duk da sassauci da shugaba Vladimir Putin yayi.
WASHINGTON D.C. —
Dubban mutane ne suka yi zanga-zangar a birninn Moscow, rahotanni kuma na cewa an gudanar da zanga zangar a biranen kasar akalla 12 ciki harda St. Petersburg.
Nan da nan dai babu rahotannin hukumomi sun yi kame a wuraren zangan zangar wadanda gwamnati ta amincce a 'a gudanar da su.
A wani lamari na daban, ranar Juma'a Rasha da Eritrea, suka fadada dangantakar su ta fuskar difilomasiyya, sa'ilin da hukumomi a Moscow suka bada sanarwar zasu gina wata cibiya kan harkokin zirga zirga a ruwa a tashar jiragen ruwan Eritiriyan dake gabashin Afirka.